Wannan shiri zai rage tsadar jigilar mai tare da taimaka wa kananan masana’antu da kamfanoni sama da miliyan 42 wajen rage kudin gudanarwa inji matatar.
A watan Agusta ne kamfanin na tace mai ya karɓi rukuni na farko daga cikin motoci 4,000 da ke amfani da CNG, wadanda za su yi aikin jigilar mai kai tsaye daga masana’antar.
Dangote ya bayyana cewa manufar wannan tsarin ita ce rage dogaro da masu jigilar mai na waje da kuma tsadar da ke tattare da hakan.