Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa ‘yan siyasa da dama suna shirin neman tikitin shugaban ƙasa a 2027, kuma ba wai fitattun mutanen da aka sansu ba.
Da yake hira da manema labarai mataimakin mai ba da shawara kan harkokin shari’a na PDP na ƙasa Okechukwu Osuoha, ya faɗa wa manema labarai cewa jam’iyyar ta na gudanar da tattaunawa da shawarwari a ɓoye domin gano wanda zai iya zama ɗan takara mai karɓuwa a fadin ƙasar.
Ya ce, mutane kamar tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP Peter Obi, da gwamnan Oyo, Seyi Makinde kadan ne daga cikin mutanen da ke aiki a bayan fage.
Ya kara da cewa yanzu abinda yafi muhimmanci a PDP shi ne tattaunawa da shawarwari da zummar neman ɗan takara da zai iya haɗa kan al’umma da samun goyon bayan ‘yan Nijeriya baki ɗaya.