Tsohon kyaftin din Manchester United kuma wanda ya fi zura kwallaye a tarihin kungiyar Wayne Rooney, ya bayyana cewa ƙungiyar ta ƙara lalacewa a ƙarƙashin mai horaswa Ruben Amorim.
Rooney ya yi waɗannan kalamai ne bayan Manchester United ta sha kashi da ci 3-0 a hannun Manchester City a wasan makon da ya gabata a gasar Firimiya ta kasar Ingila.
Ya ce duk da cewa ya na son ya nuna goyon baya ga kocin da ’yan wasan, amma babu wani alamar cigaba da ake gani a cikin tsarin kungiyar.
Ya kara da cewa babu wani tsarin da ke nuna za a samu sauyi a kungiyar nan gaba, kullum al’amura ƙara tabarbarewa suke.