Sarkin Kano na 15, kuma tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Muhammadu Sanusi II, ya nuna damuwa kan yadda gwamnatin tarayya ke ci gaba da ciyo bashi ba tare da tsari ba.
Sarki Sanus ya yi wannan bayani ne a bikin Kano International Poetry Festival KAPFEST a Kano, inda ya ce bashin da ake bin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 150 a farkon shekarar 2025 zai iya jefa ƙasar cikin mummunar matsalar kuɗi nan da shekaru 20.
Sarki Sanusi ya yi gargadi cewa idan ba a yi amfani da wadannan makudan kudade wajen inganta ilimi da ƙarfafa matasa ba, abin ba zai yi wa kasar kyau ba.
Ya kuma ce maimakon duk waɗannan basussukan a yi amfani da su ne wajen koyar da matasa domin su ne za su biya shi, amma abin takaici ana cin bashin ba tare da saka hannun jari ba.
Sai dai ya yaba wa matakin cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ceci ƙasar daga fadawa matsalar tattalin arziki.