Sakataren gwamnatin Najeriya George Akume ya baiyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi himma wurin magance matsalar rashin aikin yi da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Akume, a lokacin da sabbin shugabannin kungiyar matasa ta Nijeriya NYC, ƙarƙashin jagorancin Kwamared Jethro Annum suka kai masa ziyara a Abuja ya jaddada cewa shugaban kasa ya ƙaddamar da manufofi da tsare-tsaren da za su rage radadin rayuwa tare da samar da damar ci gaba ga matasa.
Ya ce gwamnatin su ta na da kyakkyawar alaka da matasa kuma za su ci gaba da tallafawa matasa a dukkan harkoki, ciki har da samar da sakatariyar da ta dace da kayan aiki domin sauƙaƙa wa matasan wajen jagoranci da wayar da kan sauran matasa a fadin Nijeriya saboda su amfana da shirye -shiryen gwamnatin.