Ƙungiyar Shugabannin Hukumomin Jin Dadin Alhazai ta Jihohin Nijeriya ta bukaci hukumar kula da aikin hajji ta Nijeriya (NAHCON) da ta gaggauta kammala daidaita bayanan kuɗaɗen da aka kashe Hajjin 2025 kafin ta shiga cikakken shirin na 2026.
A cikin wata wasiƙa da Shugaban ƙungiyar, Ahmed Idris Al-Makura, da Sakataren ƙungiyar, Abubakar Salihu, suka sanya hannu, sun yaba da yadda NAHCON ke haɗa jihohi a shirin hajji, amma sun nuna damuwa game da jinkirin maidawa mahajjata kuɗaɗensu da kuma wasu hakkoki.
Ƙungiyar ta ce akwai mahajjata da suka daɗe sama da shekaru biyu ana riƙe musu kuɗi, abin da zai iya kawo cikas wajen haɗa waɗanda aka jinkirta zuwa tsarin Hajjin 2026.
“Ba daidai ba ne a buɗe lissafin hajjin 2026 ba tare da rufe na 2025 ba. Wannan na iya haifar da ruɗani da wahalar aiki,” in ji ƙungiyar.
Jaridar Independent Hajj Reporters of Nigeria ta ruwaito kungiyar na yin kira ga NAHCON da ta gaggauta biyan kuɗaɗen mayarwa da sauran hakkoki, domin hakan zai ƙarfafa ikon jihohi wajen bin ƙa’idojin Hajjin 2026 yadda ya kamata.