Wata kungiyar mabiya addinin kirista mai suna “The Concerned Christian Youth Forum” ta soki sabuwar dokar da gwamnatin Neja ta kaddamar, ta tantance wa’azi ga malamai kafin hawa mumbari.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana dokar a matsayin cin zarafi da kuma tauye hakki.
Gwamna Bago dai ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin ne domin kaucewa duk wani wa’azi da ka iya tayar da fitina.
Sai dai kungiyar ta ce dokar ta ci karo da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya, na ‘yancin tunani da kuma addini.



