Hadimin shugaban Najeriya Daniel Bwala, ya ce dan gidan shugaban Seyi Tinubu ya kai matsayin da zai iya neman takara a kowane irin mukamin siyasa a Najeriya, ciki kuwa har da kujerar shugaban kasa.
Yayin wata tattaunawa da shi da aka wallafa a kafar YouTube, Bwala ya ce batun da ake yi na cewa Seyi ya samu daukaka ta sanadiyyar mahaifinsa ba gaskiya bane, yana mai bayyana shi a matsayin jajirtacce.
Kazalika ya ce Seyi Tinubu ya kasance mutum mara girman kai, domin baya kallon girma ko matsayin mahaifinsa yayin gudanar da al’amuransa, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.



