Ministan Abuja Nyesom Wike ya bayyana cewa ba karamar sa’a dan gwagwarmaya Omoyole Sowore ya yi ba, na samun shugaban Najeriya Bola Tinubu a matsayin mutum mai mutunta doka.
Yayin kaddamar da wata hanya a birnin Abuja, Nyesom Wike ya ce da wani ne ke shugabantar Najeriya ba Tinubu ba, da Sowore ya gane kurensa, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Wike ya ce kalmar da dan gwagwarmayar ya yi amfani da ita kan Tinubu a shafukan sada zumunta a kwanakin baya ta yi tsauri, yana mai cewa ko a kasashen waje irin haka ba ta faruwa.
Wannan ya zo ne daidai lokacin da ake ci gaba da dambarwa tsakanin hukumar tsaron farin kaya a Najeriya DSS da dan gwagwarmayar, kan wasu kalaman sukar Tinubu da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta.



