DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kotu ta dage sauraron shari’ar Farfesa Usman Yusuf zuwa 19 ga watan Nuwamba

-

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage sauraron shari’ar tsohon shugaban hukumar inshorar lafiya ta ƙasa (NHIA), Farfesa Usman Yusuf, zuwa ranakun 19 da 20 ga watan Nuwamba, domin cigaba da shari’a kan tuhumar da ake yi masa da cin hanci da rashawa.

Mai shari’a Chinyere Nwecheonwu ta ɗage zaman ne bayan kammala tambayoyin ga shaida na farko daga bangaren masu shigar da ƙara.

Google search engine

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tun da farko, shaidar wanda shi ne tsohon darakta a NHIA, Attahiru Ibrahim, ya amince cewa shi ne ya rubuta ƙorafi zuwa hukumar EFCC akan Yusuf a lokacin da yake shugabancin NHIA. Amma rashin lafiyar da ya samu ya sa ba a cigaba da shari’ar a jiya ba.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Yusuf a kan tuhuma biyar da suka shafi: karkatar da kudade, amfanar da kansa ta hanyar amincewa da siyan mota, yayin da Farfesa Yusuf din ya ƙi amincewa da laifukan da ake tuhumar sa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Babu adawa a jihar Plateau a zaben 2027 – Caleb Muftwang

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang, ya bayyana cewa zuwa zaben 2027 jam’iyyarsa ba za ta samu adawa a jihar ba. Ya fadi hakan ne...

Obasanjo ya musanta rubuta sanarwar mutuwarsa

Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya musanta wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya fitar da sanarwar mutuwarsa. Rubutun...

Mafi Shahara