Wani bincike da masana lafiyar kwakwalwa suka gudanar ya nuna cewa bugun yara kanana na haddasa musu fadawa cikin tsananin damuwa.
Jaridar punch ta ambato likitocin kwakwalwa na cewa daukar matakin bugu da wasu nau’ikan horo ba gyara tunanin yaran ta ke yi ba, illa haddasa musu damuwa ta lokaci mai tsayi.
Kazalika kwararrun likitocin sun bayyana damuwa kan irin bugun da ake yi wa yara a wasu lokutan da sunan cire musu shaidanu.



