Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa fursunoni 68 sun samu nasara a jarabawar NECO ta shekarar 2025.
Mai magana da yawun hukumar a jihar, CSC Musbahu Lawan, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano a ranar Litinin.
Ya ce wannan nasara ta samu ne sakamakon ingantaccen tsarin koyarwa na cibiyar gidajen gyaran hali da kuma cikakken tallafin gwamnatin Jihar Kano.
A cewarsa, shirin ya nuna yadda ake aiwatar da dokar Correctional Service Act ta shekarar 2019, wacce ta bai wa fursunoni damar koyon karatu da sana’o’i a gidajen yari.



