Rundunar ƴan sandan jihar Neja ta kama mutane 12 kan zargin sacewa tare da lalata kayan da kimarsu ta kai Naira biliyan 4.8 a tashar wutar lantarki ta Kainji.
Haka kuma ta samu nasarar cafke wasu mutum biyu kan zargin shirya karbar kudaden fansa har Naira miliyan 7.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Neja SP Wasiu Abiodun ya fitar, ya ce lamarin ya samo asali ne bayan da wani kamfani ya shigar da kara kan zargin wani jami’in tsaro da ke aiki a tashar wutar lantarkin.
A cewar sa, tun da jimawa wadanda ake zargi suka fara shirin gudanar da satar.
Sanarwar ta ce an aikata laifukan ne a lokuta mabambanta, kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kafin gurfanar da wadanda ake tuhuma a gaban shari’a.



