Kungiyar masu defo defo da kasuwancin man fetur ta Najeriya DAPPMAN ta bukaci matatar man Dangote ta bullo da tsarin da zai bai wa ‘yan kasuwar man damar samun sa a farashi mai sauki.
Da yake tattaunawa da gidan talabijin na Channels, mai magana da yawun kungiyar ta DAPPMAN Ikem Ohia, ya ce samun hadin gwiwa da kamfanin na Dangote zai tabbatar da wadatuwar man fetur a fadin Najeriya.
Ya kuma ce babu wani rikici da ke tsakanin su da matatar, yana mai cewa burin su shi ne ‘yan Najeriya su huta da fuskantar dogayen layuka a gidajen mai.



