Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya jinjinawa Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya Natasha Akpoti Uduaghan, bayan komawar ta zauren majalisar dattawan Najeriya.
A cewar Atiku, hakan na nuni da cewa ‘yan Najeriya za su iya yakar tauye musu hakki ne kawai ta hanyar hada kawunansu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wannan ya biyo bayan kai ruwa rana da aka yi tsakanin sanatar da kuma shugabancin majalisar, bayan dakatar da ita kan wasu zarge-zarge.



