Sanata Nelson Effiong ya zama Dagacin kauyen Eyo Usotai a karamar hukumar Oron ta jihar Akwa Ibom. Ya dai yi Sanata daga 2015-2019. Kafin nan sai da ya yi kakakin majalisar dokokin jihar.
Barayin daji sun taba sace Sanatan a shekarar 2021, sai da ya kwashe kwanaki 50 kafin su sako shi.