Shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa tu’annati EFCC, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa duk da ƙoƙarin da suke na yakar cin hanci, ana dawo musu ta wata sigar da hukumar ba za ta ja da baya ba wajen kare tattalin arzikin ƙasa daga masu aikata laifukan da suka shafi kuɗi.
Olukoyede ya yi wannan bayani ne a taron wayar da kai tsakanin kungiyoyi da ‘yan jarida wanda hukumar ta shirya a Abuja, inda ya samu wakilcin jami’in hulda da jama’a na hukumar Wilson Uwujaren.
Daily Nigerian ta ruwaito shi yana cewa hukumar ta ɗauki haɗin kai da fahimtar juna tare da masu ruwa da tsaki a matsayin ginshiƙin nasarar yaƙi da laifukan tattalin arziki da rashawa.
Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da jajircewa wajen haɗa kai da jama’a domin tabbatar da samun cikakken goyon bayan al’umma a fagen yaƙi da rashawa.



