Gwamnatin jihar Katsina ta kori ma’aikatan bogi 3,488, bayan karɓar cikakken rahoton daga kwamitin tantance ma’aikata.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin ta fitar, ta bayyana cewa an tantance ma’aikata 50,172, inda ta samu 46,380 da suka cancanta, ta kuma kori ma’aikatan bogi 3,488.
Sanarwar ta ce biyo bayan daukar matakin, gwamnatin ta kwato Naira miliyan 4.6 daga hannun ‘yan damfara.
Haka kuma ta yi hasashen samun rarar Naira miliyan 453.3 a kowane wata.
A cewar sanarwar mai magana da yawun Gwamnan ,Ibrahim Kaula MOHAMMED, wannan mataki zai ba ta damar mayar da hankali kan bunkasa ayyukan ci-gaba tun daga tushe.