Waɗanda aka nada din su ne Isah Ali a matsayin Sakataren masarautar Katsina da Ibrahim Abubakar a matsayin ma’aji sai Muhammad Salisu Aliyu a matsayin mai binciken kudi na cikin gida na masarautar Katsina.
Kazalika, gwamnatin jihar ta amince da nadin Gazali Muhammad a matsayin Sakataren masarautar Daura, sai Musa Yahaya a matsayin Ma’aji da kuma Ado Aliyu a matsayin mai binciken kudi na cikin gida na masarautar Daura.
Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban Sakataren ma’aikatar kula da kananan hukumomi ta jihar Katsina Malam Jamilu Yakubu da DCL Hausa ta samu kwafi.
Sanarwar ta ce hakan ya biyo bayan sanya dokar kula da masarautu ta jihar Katsina ta shekarar 2025.