Ministan man fetur na Najeriya Heineken Lokpobiri, ya ce kafin zuwan gwamnatin shugaba Tinubu, Najeriya ta shafe tsawon shekaru 10 ba tare da samun masu zuba hannun jari a bangaren ba.
A cewar ministan, hakan ya jawo mummunan koma baya a bangaren, sai dai a halin yanzu gwamnatin ta fara daukar matakan jawo hankalin masu zuba jarin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ministan ya bayyana haka ne ta cikin wata sanarwa da hadimarsa Nneamaka Okafor ta fitar, inda ya ce zuwan gwamnatin Tinubu ta yi matukar bunkasa fannin na man fetur, tare kuma da jawo hankalin masu zuba jari daga sassa daban daban na duniya.