Muhammadu Sanusi II, ya yi wannan bayani ne a yayin wani taron koli da aka gudanar a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 da aka gudanar a birnin New York, ranar Laraba.
Sarkin na Kano ya ce bude kofar saka hannun jari daga ‘yan kasuwa shine ginshiƙin da zai buɗe damar Tattalin arzikin ƙasar da kuma ci gaba da tabbatar da sauye-sauyen da ake yi a halin yanzu.
Rahoton jaridar Punch ya Ambato shi yana bayyana cewa dole ne a baiwa ɓangaren masu zaman kansu muhimmiyar dama wajen habbaka ci gaba da jawo hannayen jarin da ake buƙata don sauya Tattalin arzikin ƙasar.
Taron, wanda aka yi wa taken “ƙarfafa zuba jari don ci gaba da musayar al’adu,” ya gudana ne a dakin taro na Henry George School of Social Science da ke Manhattan, Amurka, karkashin wata sanarwa da shugaban jam’iyyar APC reshen Amurka, Farfesa Tai Balofin, ya fitar ranar Laraba.