Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun ta sun yi ajalin ƴan ta’adda da dama, sun kuma kama akalla mutum 120 tare da kubutar da mutane 41 da aka yi garkuwa da su a fadin ƙasar cikin mako guda.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis.
Ya ce hare-haren da aka gudanar tsakanin 14 zuwa 22 ga Satumba sun shafi Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Gabas.
Manjo Janar Kangye ya jinjinawa dakarun sojin kasar, bisa jajircewa da ƙwarewa da suke nunawa, tare da kira ga al’umma da su ci gaba da bai wa sojoji sahihan bayanai a kan lokaci.



