Jaridar Punch ta ruwaito cewa ana kammala kakar wasa ta bana a gasar MLS ta Amurka, dan wasan zai sanar da rataye takalmansa a hukumance.
Busquets mai shekaru 36, wanda yanzu haka ke taka leda a kungiyar Inter Miami ta Amurka, ya bai wa tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona gagarumar gudunmawa a lokacin da yake buga mata wasanni.
Ya buga wasanni da shahararrun ‘yan wasa irin su Lionel Messi, Andres Iniesta da kuma Xavi Hernandez.