Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa sama da ‘yan Nijeriya 3,000 ne ke aiki a matatar duk da sake fasalin ma’aikatanta da ta yi.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, matatar ta yi watsi da rahotannin korar dumbin ma’aikata, tare da bayyana cewa sake fasalin ya shafi wasu kalilan ne wanda ta ce ya zama wajibi don magance zagon kasa da ake yi mata.
Ta ce sama da ‘yan Nijeriya 3,000 na ci gaba da aiki a matatar man fetur din a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da daukar hazikan ‘yan Nijeriya ta hanyar shirye shiryen horar da daliban da suka kammala digiri.