Tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya zargi cewa a cikin watanni shida kacal, wanda ya gaje shi Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu fiye da rabon kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta bai wa Kano a duk tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki.
Bayan taron masu ruwa da tsaki, Ganduje ya diga alamar tambaya kan nasarorin da Abba Kabir Yusuf ya cimmawa, yana zargin cewa gwamnatin NNPP a Kano tana kashe kuɗaɗe ba tare da tsari ba.
Gandujen ya ce lokacin da ya karɓi mulkin jihar Kano a 2015, bai ɓata lokaci wajen binciken wanda na gada ba. Ya cigaba yana cewa mulki ba ya ƙarewa da gwamnati ɗaya. Amma Abba Yusuf ya fara gwamnatinsa da bincike-bincike.
Duk kan batun binciken, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya bugi kirjin cewa, a fada masa tun da aka fara binciken, me aka gano?
Sai ma ya yi kalubalen cewa gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf ta samu kuɗi a cikin watanni shida fiye da abin da gwamnatinsa ta samu a shekaru takwas, ya yi zargin cewa ba su tsinana wa jihar komai ba.
Ganduje ya kuma zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta NNPP da cewa gwamnati ce ta ramuwar gayya kuma marar tsari.
Sai dai, da jaridar Daily Trust da ta wallafa wannan labarin ta tuntubi mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ta ce bai amsa bukatarta na mayar da martani kan zargin Ganduje ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.



