An shiga sabon rikici tsakanin ƙungiyar ma’aikatan man fetur ta PENGASSAN da kamfanin Dangote Refinery, bayan da ƙungiyar ta bayar da umarnin tsunduma yajin aiki a fadin kasar sakamakon korar ma’aikata sama da 800 da ta yi zargin matatar man Dangote ta yi.
PENGASSAN ta bayyana cewa korar ɗimbin ma’aikata a kamfanin ba bisa ka’ida ba ne, tana mai cewa hakan ya saba wa haƙƙin kwadago kuma yana iya zama babbar barazana a nan gaba.
A cikin wata sanarwa,, ƙungiyar ta zargi kamfanin da korar ‘yan Najeriya saboda sun shiga kungiyar PENGASSAN, tare da maye gurbinsu da ƙarin ma’aikata ‘yan ƙasashen waje fiye da 2,000.