Rahoton binciken jaridar Premium Times ya zargi cewa ya gano tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi amfani da kujerarsa wajen karkatar da mallakar tashar Dala Inland Dry Port daga hannun gwamnatin jihar Kano zuwa hannun iyalansa da abokan sa na siyasa a jihar.
A shekarar 2006 zamanin gwamnatin Ibrahim Shekarau, jihar Kano ta mallaki kaso 20 bis 100 a tashar, inda babban ɗan kasuwa Ahmad Rabiu ke riƙe kaso 80 bisa 100 na hanun jari, wanda aka ce Jihar ta yi alƙawarin samar da ababen more rayuwa a shafin ginin tashar, amma ba ta aiwatar ba.
Sai a shekarar 2020, Ganduje ya amince da biyan Naira biliyan 2.3 daga baitul malin jihar don yin wadannan gine-gine, duk da cewa a lokacin jihar ba ta da hannun jari a cikin kamfanin.
Binciken ya ce daga baya an ƙara kwangilar zuwa fiye da Naira bilyan 4, inda aka bai wa FRI Construction Company Ltd. aikin, wacce aka danganta da tsohon ministan sufuri Abubakar Bawuro.
An tsara tashar ta Kano ne a matsayin hanyar sauƙaƙa shigo da kaya da fitar da su, domin rage jinkiri, da kuma ƙarfafa cinikayya da ƙasashen makwabta masu fama da rashin tashoshin ruwa irin su Nijar, Chadi, da Kamaru.



