Gwamnatin Najeriya ta bukaci ‘yan kasar su kara hakuri, daidai lokacin da kasar ke daf da cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai
Jaridar Punch ta ruwaito sakataren gwamnatin tarayya George Akume, na bai wa ‘yan Najeriya baki kan su kara nuna juriya musamman game da tsare-tsaren da gwamnatin shugaba Tinubu ke bullowa da su, inda ya bayar da tabbacin cewa za a ci moriyar su a nan gaba.
A cewar sa, ranar 1, ga watan Oktoba ba iya ranar tunawa da tarihi ba ce kawai, ta kasance ranar sake sabunta fata na gari ga Nijeriya.



