Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tsohon ministan yada labaran Najeriya Farfesa Jerry Gana ba shi da hurumin cewa Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugabancin Nijeriya a zaben 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito sakataren jam’iyyar na kasa Debo Ologunaba na bayyana cewa, PDP ba ta rasa nagartattun masu tsaya mata takara ba bayan Goodluck Jonathan.
Martanin jam’iyyar ya biyo bayan da Farfesa Jerry Gana, ya bayyana cewa tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan zai tsaya takarar shugabancin kasar, kuma zai kayar da gwamnatin Tinubu.



