Sojojin Najeriya karkashin rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ sun samu nasarar dakile wani hari da wasu ‘yan bindiga suka yi niyyar kai wa kan al’umma a karamar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Benue.
Wata sanarwa da mukaddashin mai magana da yawun rundunar Laftanar Ahmad Zubairu ya fitar, ta bayyana cewa dakarun sojin sun dauki matakin hana kai harin ne a ranakun 26 da 28 ga watan Satumban 2025, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun yi niyyar kai hari ne a kauyukan Agurugu da Igyudu, inda dakarun sojin suka farmake su.
Baya ga dakile harin, sun kuma samu nasarar kwato miyagun makamai daga hannun su, bayan tarwatsa su da jami’an sojin suka yi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.