‘Yan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG hudu ba za su samu damar fafata wasan da kungiyar za ta kara da Barcelona a gasar zakarun nahiyar turai ba.
Fabrizio Romano ya wallafa cewa babu sunayen shahararrun ‘yan wasan cikin tawagar wadanda za su buga wa kungiyar ta PSG wasan.
‘Yan wasan dai su ne Dembele, Doue, Marquinhos da Kvaratskhelia.
Masu ruwa da tsaki na ganin cewa rashin wadannan hazikan ‘yan wasa na iya zamewa PSG tarnaki a wasan da za ta fuskanci kungiyar ta Hansi Flick.