Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya yi wa kalaman Atiku Abubakar raddi cewa zai mara wa duk matashin da ya kayar da shi a zaben fidda gwani na 2027.
Jaridar Punch ta ruwaito Atiku Abubakar a hira da ya yi da BBC yana cewa zai janye wa matashi idan aka kayar da shi a zaben fitar da gwamnati na jam’iyyar ADC domin matasa da mata ne jam’iyyar ta sa a gaba.
Sai dai, Shehu Sani a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X ya ce, abu ne mai wahala kayar da Atiku Abubakar a zaben fitar da gwani domin kuwa rijiya ba wajen wasan yaro ba ne.