Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa wasu gwamnoni daga jam’iyyun adawa a Nijeriya na shirin komawa jam’iyyar APC domin goyon bayan shugabancin Bola Ahmed Tinubu.
A cewar wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Jackson Udom, ya fitar a Abuja, Akpabio ya yi wannan bayani ne a Owerri, jihar Imo, a yayin bikin ƙaddamar da littafin da Gwamna Hope Uzodimma ya rubuta tare da kaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da Shugaba Tinubu ya yi.
Ya ce saboda ayyukan da shugaba Tinubu ya yi a shekaru biyu da suka gabata, akwai gwamnoni da dama da suke jiran a karbesu cikin jam’iyyar APC.
Ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya sun fara jin daɗin sauye sauyen da gwamnatin Tinubu ta kawo, wanda suka taɓa rayuwar ɗalibai, manoma da ‘yan kasuwa a fadin kasar.