A daidai lokacin da Nijeriya ke murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya yi kira ga shugaba Tinubu da ya sake tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a karo na biyu.
Namadi ya yi kiran ne a lokacin da yake ziyarar ayyuka a jihar domin murnar ranar samun ‘yancin kai.
A cewarsa, mazauna Jihar Jigawa tuni suka amince Tinubu ya kara tsayawa takarar shugabancin Nijeriya sakamakon tsare-tsarensa na tattalin arziki da kuma ayukkan ci-gaba.
Gwamnan ya kara da cewa, fiye da kuri’u miliyan biyu na nan na jiran shugaba Tinubu a zaben 2027 sannan al’ummar jihar na goyon bayan shirye-shiryensa na Renewed Hope