A daren Laraba ‘yan bindiga suka yi garkuwa da kansiloli biyu tare da Limami a kauyen Tsauni da ke a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara.
Kansilolin da ke wakiltar mazabun Gidan Goga da Tsibiri da ke a karamar hukumar Maradun sun shiga hannun masu garkuwar ne a kusa da wani shingen bincike na ‘yan sanda bayan idar da sallar Magariba.
Shugaban karamar hukamar Maradun, Hwanarabul Sanusi Gama ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce, wadanda abin ya shafa suna hutawa ne a wajen mai shayi lokacin da ‘yan bindigar suka far musu.
Gama ya kuma kara da cewa, ‘yan bindigar sun fita neman wani ne da ba su same shi ba suka huce haushi kan wadanda suka yi garkuwa da su din.
Haka kuma, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni aka baza jami’an tsaro a yankin domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.



