Kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC ta Arewa ta Tsakiyar Nijeriya ta roƙi Shugaba Bola Tinubu da ‘yan majalisar dokoki ta ƙasa da kada su amince da buƙatun kafa rundunar ‘yan sanda ta jihohi a Najeriya.
Wannan kiran ya biyo bayan jawabin Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, wanda ya ce lokaci ya yi da za a samu ‘yan sandan jihohi domin magance matsalolin tsaro a jiharsa da sauran sassan ƙasar.
Sai dai a wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya fitar a Abuja, kungiyar ta bayyana adawarta ga wannan shawara, tana mai cewa kafa ‘yan sandan jihohi zai zama barazana ga dimokuraɗiyya da zaman lafiya.
Kungiyar ta ce mafi yawan gwamnonin jihohi na amfani da karfin gwamnati wajen danniya da tsoratar da ‘yan adawa da ƙananan ƙabilu, don haka idan aka ba su cikakken iko da rundunar ‘yan sanda ta jihohi, za su yi barna fiye da yadda ake gani a yanzu.
Kungiyar ta ce musamman a yankin Arewa ta Tsakiya, inda ake da ƙabilu da addinai daban-daban, kafa ‘yan sandan jihohi zai iya haifar da rigingimu.