Jam’iyyar ADC ta caccaki gwamnatin Bola Tinubu bayan rahoton Bankin Duniya da ya nuna cewa mutane miliyan 139 a Nijeriya na rayuwa cikin talauci.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce rahoton ya tabbatar da gazawar manufofin tattalin arzikin gwamnati da suka kara jefa jama’a cikin ƙunci.
Fadar shugaban kasa ta musanta hakan, tana cewa Rahoton bai nuna hakikanin halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki ba.
Sai dai, Jam’iyyar ta ADC ta zargi gwamnati da amfani da bayanan ƙarya don boye gazawarta da talaucin da ke karuwa a tsakanin ‘yan Nijeriya.



