Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da tarukan jin ra’ayoyin jama’a a mazabu uku na jihar domin shirin kasafin kudin 2026.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, taron da aka gudanar a Tambuwal, Tangaza da Gwadabawa ya haɗa sarakunan gargajiya, ‘yan majalisu, kungiyoyin matasa, mata da masu bukata ta musamman domin tantance bukatun al’umma.
Kwamishinan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Dr. Abubakar Zayyana, ya ce shirin na daga cikin manufar gwamnan jihar, Ahmad Aliyu na tafiyar da mulki a buɗe tare da tafiya da jama’a, wanda zai mayar da hankali kan bangarorin ilimi, kiwon lafiya, ababen more rayuwa da rage talauci a jihar.