Mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya amince da tattaunawa da Shugaba Bola Tinubu game da ci-gaba da tsare jagoran IPOB, Nnamdi Kanu da ake.
Sowore ya bayyana hakan ne a shafinsa na X a ranar Juma’a bayan ganawarsa da Jonathan a birnin Abuja, inda ya ce tattaunawar ta mayar da hankali kan muhimmanci da bukatar warware matsalar Nnamdi Kanu cikin gaggawa da adalci.
Sowore ya ce, Jonathan ya amince cewa akwai bukatar gaggawar magance wannan matsala cikin gaskiya da adalci, kuma ya yi alkawarin ganawa da Shugaba Tinubu don tattauna batun nan ba da jimawa ba.
Ya kuma kara jaddada kira da ya ke yi na a saki Kanu, yana mai cewa yana tsare ne saboda ya tashi tsaye wajen kalubalantar matsalar wariyar da ake zargi da yi wa wasu yankuna a Nijeriya kamar yadda Punch ta ruwaito.