Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Yamaltu/Deba a Jihar Gombe, Inuwa Garba, ya roki gwamnatin tarayya su kawo musu dauki kan hare-haren dorinar ruwa da suka addabi mazauna yankinsa.
Garba ya gabatar da wannan bukata ne a zaman da mataimakin kakakin majalisar wakilai Benjamin Kalu ya jagoranta, inda ya bayyana cewa hare-haren sun yi sanadin rasa rayukan wasu mafarauta da manoma a bakin koguna da gonaki.
Ya kara da cewa, hare-haren da ke faruwa a yankin sun haifar da tsoro da tashin hankali, abin da ya tilasta wasu manoma da masu kamun kifi barin aikinsu, lamarin kuma na kara ta’azzara talauci da rashin abinci.
A ranar 5 ga watan Oktoba, wata dorinar ruwa ta afkawa masunta a cikin kwale-kwale, inda ta kashe mutum daya mai suna Yahaya Bawa, ta kuma jikkata wasu da dama kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.