Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar Zamfara na Kaura Namoda South, Muhammad Kurya, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Kurya ya sanar da sauya shekar tasa ne a Asabar dinnan yayin wani taro da aka gudanar a birnin Gusau na jihar Zamfara.
Jaridar Punch ta rawaito cewa wannan sauyin sheka ya biyo bayan zaben cike gurbi da hukumar INEC ta ayyana Kamilu Sa’idu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
A cikin wata sanarwa da Kurya ya wallafa, ya zargi gwamnati da rashin magance matsalar tsaro lamarin da ya ce shi ne ya taimaka wajen faduwar sa zabe da kuma tabarbarewar tsaro a jihar.