Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ebonyi ta ce ta kama wani mutum mai matsakaitan shekaru mai suna Chukwuma Onwe bisa zargin sayar da ɗansa mai kwanaki biyar da haihuwa kan kudi Naira miliyan 1.5.
Bayanai sun ce, an cafke Onwe ɗan asalin garin Nwezenyi-Igbeagu da ke ƙaramar hukumar Izzi a jihar, ne bayan matar da yake shirin aura, Philomena Iroko, ta sanar da maƙwabcinta, wanda kuma ya kai rahoto ga ‘yan sanda game da abin da mijin ya aikata.
Rahotanni sun nuna cewa jaririn, an sayar da jaririn namijin ne ga wata mace mai suna Chinyere Ugochukwu, wadda ita ma ‘yan sanda suka kama.