Tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa matsin rayuwa da ake fama da shi a yanzu ya fara shafar lafiyar kwakwalwar ‘yan Nijeriya.
Obi, ya bayyana haka ne a shafinsa na X yayin bikin ranar ranar lafiyar kwakwalwa ta duniya a ranar 10 ga Oktoba.
Ya ce talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa sun sanya wasu matasa shiga cikin damuwa da aikata laifuka.
A cewarsa, rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO ya nuna cewa sama da mutane miliyan 40 a Nijeriya na fama da matsalolin lafiyar kwakwalwa, amma ƙasa da likitocin kwakwalwa 300 ne kawai ke kula da su,wannan na nuna yadda ƙasar ke nuna halin ko in kula da fannin lafiya.
Obi ya bukaci gwamnati da ta ɗauki mataki kan wannan batun na kiwon lafiya, tare da buƙatar ƙara yawan likitocin kwakwalwa da kuma samar da asibitocin kwakwalwa a kowane yanki na ƙasar.



