Nadin Farfesa Joash Amupitan SAN a matsayin sabon shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC da Shugaba Bola Tinubu ya yi, ya haddasa cece kuce a tsakanin jam’iyyun adawa, inda wasu ke ganin hakan zai tsarikan yin zabe.
Shugaba Tinubu dai ya bayyana cewa ya zabi Amupitan, ɗan asalin jihar Kogi, ne bisa cancanta mutunci da kwarewa, bayan majalisar koli ta Ƙasa ta amince da nadin nasa a ranar Alhamis, wanda ya zo bayan karewar wa’adin Farfesa Mahmood Yakubu a watan Oktoba 2025.
Sai dai yayin da ake shirin tura sunan sabon shugaban INEC zuwa majalisar dattawa domin tantancewa, shugabannin jam’iyyun adawa sun rabu gida biyu wasu na ganin nadin yana bisa doka, yayin da wasu ke ganin zai iya haifar da koma bayan siyasa a zaben 2027.
Jaridar Punch ta rawaito cewa,Sakataren rikon kwarya na jam’iyyar Labour Party,Tony Akeni, ya ce babu wata hujja ta doka da za ta hana Tinubu nada Amupitan, amma ya yi gargadin cewa hakan na iya zama cikas ga sahihancin zabe.



