Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja yau Lahadi, domin halartar taron shugabannin kasashe da gwamnatoci na Aqaba Process a birnin Rome na kasar Italiya, wanda zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a yankin Yammacin Afirka.
Kamar yadda fadar shugaban kasa ta sanar, taron zai fara ne a ranar 14 ga Oktoba, inda zai tattaro shugabannin kasashe, manyan jami’an leken asiri da sojoji daga kasashen Afirka, da kuma wakilan kungiyoyin kasa da kasa da na sa-kai, domin tattauna kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara a Yammacin Afirka.
Shugaban kasa zai tafi da tawagar gwamnati da ta hada da Ministar Harkokin Waje mai kula da bangaren kasa da kasa, Ambasada Bianca Odumegwu–Ojukwu, Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, Mai ba da shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, da Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Mohammed Mohammed, da wasu manyan jami’an gwamnati.



