Ministan ma’adanai, Dele Alake, ya bayyana cewa gwamnatin Nijeriya na shirin kafa sabuwar hukuma da za ta rika sa ido kan fitar da ma’adanai kafin jigilar su zuwa kasashen waje domin dakile ɓarnar kudaden shiga da kuma ƙara habaka tattalin arzikin kasar.
Alake ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai an Abuja gabanin taron Nigeria Mining Week karo na 10 da za a gudanar daga ranar 13 zuwa 15 ga watan Oktoba, 2025.
Hakazalika, Alake ya ce wannan sabon tsari ne da ke cikin manufofin gwamnati na tabbatar da gaskiya da cike gibi a harkokin kudaden shiga na ma’adanai.
A cewarsa, matakin na daga cikin shirin tattalin arzikin Shugaba Bola Tinubu na ƙara samun kudaden shiga bayan na albarkatun mai, ƙarfafa da’a ta ɓangaren kudi, da kuma mayar da masana’antar hakar ma’adinai daya daga cikin ginshikan bunkasar tattalin arzikin Nijeriya.