Sakamakon da ya fara shigowa daga zaben shugaban kasa na Kamaru ya nuna cewa dan takarar adawa, Issa Tchiroma Bakary, na samun nasara a yankunan da Shugaban Kamaru, Paul Biya ke da karfi a siyasance kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Shugaba Biya mai shekara 92 na fuskantar ‘yan takara tara, ciki har da tsoffin abokansa a gwamnati kamar Bello Bouba Maigari, tsohon ministan yawon bude ido, da kuma Bakary, wanda ya kasance ministan kwadago kafin ya sauka daga mukaminsa.
Biya ya kada kuri’arsa a wata makaranta a birnin Yaoundé, inda ya ki bayyana makomarsa sai bayan an sanar da sakamakon zaben a hukumance.
Rahotanni daga kwamitocin zabe na kananan hukumomi sun nuna cewa jam’iyyar Bakary, FSNC, tana samun nasara a wurare da dama kan jam’iyyar mulki ta CPDM, yayin da wasu majiyoyi suka tabbatar da cewa, Bakary na kan gaba a mazabu da dama a birnin Yaoundé.