Tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi, ya caccaki gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC, yana mai cewa babu wata kasa da za ta cigaba idan mafi yawan al’ummarta suna cikin talauci.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, Obi ya ce rahoton Bankin Duniya da aka fitar a ranar 8 ga Oktoba ya nuna cewa ‘yan Nijeriya miliyan 139 ke rayuwa cikin talauci, sabanin miliyan 87 da aka ruwaito a shekarar 2023 lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau karagar mulki.
Jaridar Punch ta ruwaito Obi yana bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ke nuna yadda al’amurran tattalin arziki ke tabarbarewa, yana mai cewa ya kamata rahoton ya zama abin tunani ba musanta gaskiyar da ke faruwa a zahiri ba.
Hakazalika ya kara da cewa, manufofin tattalin arzikin gwamnati ba su da tsari da fifita talaka, yana mai kira ga gwamnati da ta mayar da hankali kan sauye-sauyen da ke karfafa masana’antu, noma, da kuma saka hannun jari a fannin ilimi da lafiya.



