Kungiyar Movement for the Emancipation of Nigeria wato MEN, ta bukaci gwamnatin Nijeriya ta dakatar da shari’ar da ake yi wa tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, tare da sakin sa nan take.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya fitar a ranar Talata, Dalung ya ce, ci-gaba da tsare Kyari babban rashin adalci ne ganin cewa an ba wasu da aka yanke wa hukunci afuwa ciki har da masu safarar miyagun kwayoyi da masu garkuwa da mutane da daga cikin su tawagar Kyari ce ta kama.
An gurfanar da Kyari da wasu mutane 6 a gaban kotu a watan Maris 2022 bisa zargin hada baki wajen safarar kilo 21.35 na hodar-iblis da hukumar NDLEA ta kama daga hannun masu safarar miyagun kwayoyi kamar yadda Punch ta ruwaito.



