Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa duk da kira da Gwamna jihar, Abba Kabir Yusuf ya yi ga Shugaba Bola Tinubu da ya sauke shi daga mukaminsa, har yanzu alaƙarsa da gwamnan tana da kyau tare da mayar da hankali kan tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Daily Trust ta ruwaito cewa Abba ya yi wannan kira ne yayin bikin cikar Nijeriya shekara 65 da samun ‘yancin kai, inda ya koka kan rashin halartar kwamishinan a wajen taron da kuma janye jami’an ‘yan sanda daga dandalin bikin.
A yayin taron manema labarai a ofishin rundunar ‘yan sanda, CP Bakori ya ce bangarorinsu biyu na aiwatar da nauyin da kundin tsarin mulki ya dora musu, yana mai cewa babu wata matsala tsakaninsa da gwamnan.



